1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Baje kolin kayayyakin tarihin Nok ya yi nasara

April 2, 2014

Wannan baje kolin kayakin tarihin daga yankin Nok da aka yi a Frankfurt ya samu karbuwa a wurin jama'a wanda dalilinsa aka tsawaita lokacin baje kolin da wata guda.

https://p.dw.com/p/1BaPH
Nok-Skulptur - Nigeria
Hoto: Norbert Miguletz

Daga karshen watan Oktoban shekarar 2013 zuwa karshen watan Maris na wannan shekara ta 2014 a birnin Frankfurt na nan Jamus an baje kolin kayakin tarihi da aka tono a yankin Nok dake jihar Kadunan Najeriya. Wannan baje kolin ya samu karbuwa a wurin jama'a wanda dalilinsa aka tsawaita lokacin baje kolin da aka yi a gidan Liebieghaus da wata guda.

A cikin abin da aka kira baje koli na musamman da aka wa taken Nok asalin kayakin tarihi na Afirka, a gidan baje kolin kayakin tarihin na Liebieghaus da ke birnin na Frankfurt aa kwashe tsawon watanni biyar ana baje kolin kayakin tarihi da aka tono a yankin na Nok da ke arewacin Najeriya. Wannan dai shi ne karon farko da aka baje kolin kayakin tarihin na fiye da shekaru 2000 na al'adun gargajiyar al'umar Nok. Masana ilimin hako kayan tarihi na jami'ar Frankfurt tare da hadin guiwar takwarorinsu na Najeriya da ke karkashin hukumar kula da kayan tarihi ta Najeriya suka kwashe kimanin shekaru takwas suna aikin hako kayakin a sassa daban daban na Nok.

Aikin hadin guiwa tsakanin Jamus da Najeriya

Yusuf Abdallah Usman
Yusuf Abdallah Usman shugaban hukumar adana kayakin tarihi ta NajeriyaHoto: DW/M. Nasiru Awal

Yusuf Abdallah Usman, shi ne shugaban hukumar adana kayan tarihi ta Najeriya ya yi mana karin haske da cewa: "Kayakin da aka baje kolinsu kayaki ne da aka hakosu a sassa daban daban na yankin Nok. An hakosu ne sakamakonn hadin guiwa tsakanin hukumata da kuma jami'ar Frankfurt da ke Jamus. Masana masu ilimin hako kaya a kasa da suke nazari a wannan jami'a da kuma nawa masanan da suke aiki a karkashin hukumata, su ne suka hadu suka yi wannan aiki."

Farfesa Peter Breunig na jami'ar birnin Frankfurt shi ya jagoranci masana daga Jamus wajen aikin tono kayakin tarihin na Nok, ya yi bayani ga yadda Nok din ya janyo hankalinsu, inda ya ce. "Mun kwashe shekaru 15 daga a 1989 muna yi wa hukumar bincken kimiyya ta Jamus aiki a yankin tafkin Chadi, inda muka gano dadaddun kayakin tarihi na musamman. Daga nan muka fara tunanin fadada bincikenmu. A lokacin wato shekarar 2005 al'adun Nok sun yi fice saboda kayakinsu na musamman. Kuma duk wanda ya ga wadannan kayaki na fasahar ya san cewa ba manoma ne suka yi su cikin dare daya ba. Kayaki ne da suka kunshi na dauloli da fadojin sarakuna da ke bayanin ci-gaban wasu al'adu."

A shekaru gommai na 1940 ne dai kayakin tarihin na Nok ya dauki hankalin Bernard Fagg masanin aikin hako kayakin tarihi a karkashin kasa na Birtaniyya. An gano kayakin farko ne lokacin aikin hakan karfe a yankin. Tare da taimakon mahaka kafin karshen shekarun 1970 Fagg ya tattara burabusan kayakin tarihi fiye da 150 na yankin Nok.

Skulpturen der Nok-Kultur Ausgrabung in Ifana Nigeria
Masu aikin tono kayakin tarihi a IfanaHoto: Goethe-Universität Frankfurt

Su kuma a lokacin aikinsu na shekara shekara da suka kwashe watani suna yi, masu bincike daga Frankfurt sun yi hadin guiwa da hukumar kula da kayakin tarihi ta Najeriya da jami'o'in Ahmadu Bello ta Zaria da kuma ta Jos. Sai dai masu sukar lamiri sun yi korafin karancin gudunmawa daga bangaren Najeriya, zargin da shugaban hukumar adana kayan tarihi ta Najeriya Yusuf Abdallah Usman ya ce bai da tushe bare makama.

Babbar nasara ga baje kolin

Farfesa Vinzenz Brinkmann shi ne shugaban tattara kayakin tarihi a gidan baje kolin kayan tarihi na Liebieghaus a Frankfurt ya ce saboda nasarar da baje koli yayi, ya sa aka tsawaita lokacin nune-nunen.

"Baje kolin ya samu babbar nasara. Mun kasance a sahun farko a tsakanin gidajen baje kolin kayakin tarihi a Frankfurt saboda kayakin daga Nok sun kasance tamkar maganadisu da ke jan hankalin jama'a. Martanin da muka samu na yabo daga maziyarta ya sa mun tsawaita lokacin baje kolin. Muna kuma farin ciki da duk wani martani da muka samu."

Yanzu haka dai ma'aikata daga hukumar adana kayakin tarihi ta Najeriya suna a birnin na Frankfurt suna sa ido yadda ake harhada kayakin da za a mayar da su Najeriya nan ba da jimawa ba. Hukumar a cewar shugabanta Yusuf Abdalla Usman ta yi tanade-tanade don hana wadannan kayaki masu daraja fadawa hannun bata gari.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Zainab Mohammed Abubakar