Badakalar mai ta jawo kace-nace a Ghana
July 5, 2017Ministan kula da makamashin kasar Boakye ne ya sanar da rusa kwamitin bayan da ya ce hukumar bincike ta kasa BNI da kuma hukumar tsaro duk sun wanke Manajan kamfanin man Alfred Obeing Boateng daga zargin da ake masa na hannu a kan badakalar gurbata mai da gangan a ma'aikatar man kasar.
Ana dai ci gaba da cece-kuce kan wannan mataki da ministan ya dauka, wani abu da ya daure wa al'umma da dama kai, shi ne ko mai ya sa ministan ya riga malam masallaci ganin yadda ya yi saurin yanke hukunci na rusa kwamitin don tsayara daina binciken, Dan majalisa Hon Dakora ya yi bayani da cewa
‘‘Ga shi a zahiri cewa shugaban kamfanin ya aikata ba daidai ba, mene ne Ministan ke yin rufa- rufa, wannan hanya ce ta kauce wa shari'a daga cin hanci da aka aikata, kamata ya yi a bar kwamitin da aka kafa ta yi aikinta ta kuma fito da sakamakon binciken, ga dai gwamnati mai ikrarin kawar da cin hanci, wannan mataki ya kara jadada kalamun da ya fito daga bakin dan jam'iyyarsu Kennedy Agyapong da ya ce idan aka salammi shugaban, to zai tona asirin yadda jam‘iyyar ta ci zaben shekarar 2016‘‘
A daya bangaren kuwa akwai wasu da ke ganin ya kamata shugaban kamfanin ya ja da baya don bai wa hukumomi damar gudanar da bincike, Mr Mensah na jam'iyyar NPP shima dai ya bayyana ra'ayinsa yana mai cewa
‘‘Menene dalilin da ya sa zai ja da baya a gudanar da bincike a kan man fetur da aka gurbata, ai harkoki na cikin gida da tsarin aikin ma'aikata na masu bincike ne ba wai na shugaba ba, Ya aka yi aka gurbata man fetur‘‘
A halin yanzu dai za a iya cewa hankula sun fi karkata zuwa ga yanda gwamnatin Nana Addo za ta fidda kanta daga cikin wannan badakalar man fetur da kuma zargin yin sama da fadi da kudin kasar Miliyan 7.
Ana dai zargin shugaban kamfanin man da wasu na kusa da shi da gurbata man kamfanin da gangan da sayar da shi da rahusa da zummar cin kazamar riba.