Ba shiga ba fita a fadar shugaban kasar Nijar
July 26, 2023Rahotannin da ke fitowa daga Jamhuriyar Nijar, na cewa sojojin da ke gadin fadar shugaban kasar sun garkame ko'ina, inda bayanai ke nuna cewa suna rike da Shugaba MMohamed Bazoum a halin da ake ciki.
Haka nan ma sojojin sun toshe dukkanin hanyoyin da ke kai mutane ma'aikatun gwmanatin kasar da ke kusa da fadar shugaban kasar da safiyar wannan Laraba.
Majiyoyi daga fadar Shugaba Bazoum dai sun cewa hatta sauran ma'aikata da ke aiki a ofishi ba kyale su domin shiga harabar ba a yau.
Matakin sojojin na Nijar ya zo daidai da wanda sojojin juyin mulki suka dauka a kasashen da ke makwabtaka da Nijar din a baya-bayan nan.
Nijar din dai ta fuskanci wani yunkurin juyin mulki cikin watan Maris na 2021 kwanaki kalilan kafin a rantsar da Shugaba Bazoum.
Al'uma a sassa na Yamai babban birnin kasar ta Nijar dai na gudanar da harkoki yadda aka saba, kuma ba a katse hanyoyin sadarwa ba.