010811 Ramadan Muslime Fasten
August 3, 2011A ranar Litinin al'umar Musulmai a ko-ina cikin duniya suka tashi da azumin watan Ramadana, inda za su kwashe tsawon wata ɗaya suna kame bakinsu da dai sauransu tun daga hudowar alfijir zuwa faɗuwar rana. To sai dai ga musulmi kimanin miliyan huɗu a nan Jamus azumin na bana ya zo musu a lokacin zafi na bazara, inda rana ta fi dare tsawo. Wato suna fara kame bakinsu daga misalin ƙarfe huɗu na asuba izuwa ƙarfe tara da rabi na dare lokacin da rana ke faɗuwa, wato kusan sa'o'i 18. To sai dai duk wanda ya zanta da Musulmi zai ji suna nanata cewa watan Ramadana ba azumin ne kaɗai ya ƙunsa ba, yana tattare da wasu shirye-shirye da dama, musamman a unguwar Bad Godesberg a nan birnin Bonn inda mafi yawan Musulmi birnin su kimanin dubu 30 suke da zama. Shirin na wannan mako ya ziyarci wasu ɗalibai ma'aurata a unguwar ta Bad Godesberg inda ya ga yadda yanayin azumun yake a tsakaninsu.
A wani shagon sayar da kayan abinci na Musulmi dake a Bad Godesberg, a nan ne Salma da mijinta Yamen suke cefane.
“A nan haka dabino ne, wanda shi ne abin farko da ya kamata a yi buɗe baki da shi. A nan ɓangaren dabino ne daga ƙasar Tunisiya, ana ƙara musu kayan zaƙi, daga can haka kuma na ƙasar Iran ne, sun fi daɗi, su muke saya.”
Kwandon cefanen Salma sai nauyi yake ƙara yi saboda kayan abincin da take saye na azumi. Sai dai tana da mataimaka wato mijinta Yamen da kuma ɗanta Ahmed Said mai shekaru 4 da haihuwa.
Hannu ɗaya ba ya ɗaukar jinƙa
Ahmed ɗin ya faɗawa mahaifiyarsa cewa shi ma a shirye yake ya taimaka wajen dakon kayan cefanen daidai da mahaifinsa Yamen, wanda ya yi ƙarin bayani da cewa a kullum yana jin daɗin taimakawa matarsa a aikace aikacen gida.
“Dole ka taimakawa matarka a cikin watan azumin Ramadana domin ita tana azumi. Ina jin daɗin shiga kicin in taimaka. To sai dai a wasu lokutan matan ba sa ƙaunar ganin maza a kicin saboda wai muna kawo musu ciƙas. Su kan kore mu daga cikin, amma duk da haka wani abin sha'awa ne ka taimakawa matarka wajen girki.”
Har yanzu dai Salma tana cikin shagon tana ci gaba da cefanen.
“Nan haka nama ne kala-kala, amma na fi son naman rago. Yanzu sai mu yanka da inji.”
Sai dai yawan naman da Salma ta yanka da inji kuma ya faɗa a jakar ledarta ya yi kilogramm da dama, wato yayi yawa matuƙa fiye da yawan iyalin gidanta, to amma da yake akan samu baƙi na ba zato ban tsammani, Salma ba ta damu da yawan naman ba.
“A kullum muna maraba da baƙi dake kawo mana ziyara. Su kan bugo mana waya kai tsaye su sanar da mu cewa suna hanya, ba tare da farko mun shirya da zuwansu ba. Suna zuwa mu yi buɗe baki tare.”
Wannan dai ba baƙon abu ne a cikin watan Ramadana a wannan gida, inji mijin Salma, Yamen a cikin murmushi, yayin da ɗansu Ahmed ke wasa yana murɗa wani akwatin rediyo.
Watan azumi dama ne na ƙarin ayyukan ibada
Yamen ya ci-gaba da cewa watan azumin Ramadana wani lokaci ne na haɗuwa tare a ci abinci a kuma yi ibada tare. Dole ne mai ƙarfi ya taimakawa marasa ƙarfi.
“Idan kana jin yunwa za ka fi gane irinn wahalar dake tare da ita. Yunwa ba ta da kyau ko kaɗan. Saboda haka muke ƙoƙarin taimakawa waɗanda ba su da shi. Aiki ne mai kyau ƙwarai ka dafa abinci ka ba wa wasu.”
A saboda haka Yamen da Salma sukan taimaka a masallaci inda a kowane maraice ake dafa abinci na gama gari domin yin buɗe baki tare. A banan Yamen ya ƙuduri aniyar burge wasu Jamusawa a lokacin buɗe baki, saboda haka ya shirya gayyatar wasu ɗalibai 200 zuwa gidansa cin abinci yamma a cikin wannan wata na Ramadana. Har yanzu dai ma'auratan biyu wato Yamen da Salma suna karatu a jami'a. Yamen na mai ra'ayin cewa ba azumi kaɗai watan Ramadana ya ƙunsa, ya kuma ƙunshi ayyukan alheri daban daban.
“Duk wasu abubuwan marasa kyau da ka yi a baya, ya kamata ka bar su yanzu. Yi da wani, ko furuta kalmomi banza suna daga cikin manyan zunubai da suke yi da wuyan bari. Amma ai rashin cin abinci da shan ruwa ba su ne babbar matsalar ba, wani lokacin kana jin daɗin kame bakin ne.”
Salma da Yamen da ɗansu Ahmad Said sun ci-gaba da tattaki a gaban shagunan Larabawa dake a unguwar ta Bad Godesberg waɗanda dukkansu suka cika da kayan azumi.
Watan azumi: ƙarin ciniki ga kantunan Musulmi
Wani yaro mai suna Hakam sanye da rigar wasan motsa jiki, yana taimakawa mahaifinsa a shagon sayar da abinci irin na Larabawa. Hakam ɗan shekaru 12 da haihuwa, ya ce a bana ya fara azumin na watan Ramadana. Shin ko da wuya?
“Ba matsala. To sai dai idan kana wasan motsa jiki za ka bukaci shan ruwa amma ba za ka iya ba saboda azumi. Saboda haka a lokacin azumi ba na aiki da yawa, na fi son in yi zama na a gida in yi wasan game, musamman Playstation.”
Shi kuwa mahaifin Hakam ya duƙufa ne wajen shirya wani kalaci na musamman a lokacin azumin.
“Wannan miya ce da nama da salad da kayan ƙwalama. A wannan lokaci na azumi wannan gidan abinci na cika da jama'a. Wannan lokaci ne na ciniki.”
Ko shakka babu wani haɗin abinci a Ramadana akan ƙayyadadden farashi ciniki ne mai kyau. Sauran gidajen abinci a unguwar ta Bad Godesberg suna irin wannan haɗi idan suke buɗewa har ƙarfe biyun dare musamman ga Larabawa ‘yan yawon buɗe ido domin duba lafiyar su.
Mawallafa: Miriam Klaussner / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Ahmad Tijani Lawal