1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ayar tambaya game da tsige Ndume da majalisa ta yi

Uwais Abubakar Idris MAB
July 18, 2024

Matakin da majalisar dattawan Najeriya ta dauka na tsige Sanata Ali Ndume daga mukaminsa na mai tsawatar wa majalisa saboda ya soki shugaban kasa Bola Tinubu ya sanya nuna damuwa a kan makomar dimukuradiyyar kasar.

https://p.dw.com/p/4iTHz
'Yan majalisa sun saba daukar matakan ladabtarwa a Najeriya
'Yan majalisa sun saba daukar matakan ladabtarwa a NajeriyaHoto: Nigeria Office of the House of Representatives

Shugaban majalisar dattawan Najeriya Sanata Godswill Akpabio ya buga gudama har sau uku domin tabbatar da tsige Sanata Ali Ndume biyo bayan kalaman da ya furta na sukar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu. Dana majalisar ya ce wasu sun kange shi Shugaban kasa, don haka bai san zahirin abin da ke faruwa a kasar ba,  Wadannan kalaman da ba su yi wa jamiyyarsa ta APC mai mulki dadi ba , ya sanya ta rubuta wa majalisar tare da nuna bacin ranta, abin da ya sanya shugaban majalisar datawan Godswil Akpabio jagorantar tsige shi ba tare da bata lokaci ba.

Ndume ya saba fuskantar tsigewa daga majalisa

Sukar Shugaba Bola Tinubu ya sa majalisar dattawa ladabtar da Ali Ndume
Sukar Shugaba Bola Tinubu ya sa majalisar dattawa ladabtar da Ali NdumeHoto: Ubale Musa/DW

Abin da ya fi daga hankali shi ne, jamiyyuarsa ta APC ce ta bai wa majalisar umurnin tsige Sanata Ndume inda majalisar cikin hanzari ta dauki matakin duk da cewa Sanatan bai hallarci zamanmajalisar dattawa ba domin an yi mashi rasuwa inda ya tafi jiharsa ta Borno, Watanni kalilan bayan da majalisar ta dauki irin wannan mataki ga Sanata Abdul Ningi sakamakon sukan shugaban Najeriyar. Wannan na nuna tamkar zunubi ne a soki shugaban Najeriya ko da kuwa ya yi ba daidai ba? Farfesa Abubakar Umar Kari masanin kimiyyar siyasa a  jami'ar Abuja ya ce wannan abin mamaki ne.

Tasgaro a fannin fadan albarkacin baki?

A tsarin dimukuradiyya dai, kowane dan kasa ko yana a jamiyya mai mulki ne na da ikon fadin albarkacin bakinsa musamman a kan abubuwan da gwamnati ke yi. Ga dan majalisa ma shi ne ya fi samun wannan iko a tsarin mulki.

Majalisun baya ma sun dauke matakin tsige ko dakatar da 'yan majalisun Najeriya
Majalisun baya ma sun dauke matakin tsige ko dakatar da 'yan majalisun NajeriyaHoto: Getty Images/AFP/K. Sulaimon

Tuni jamiyyun adawar Najeriya suka maida murtani a kan lamarin. Dr Yunusa Tanko shi ne jami'in yada labaru na dan takarar neman shugabancin Najeriya a zaben 2023 Peter Obi. Sanata Ali Ndume ya saba da irin wannan kalubale a majalisa domin ko da a 2017 sai da majalisar datawa ta tsige shi daga mukaminsa na shugaban masu rinjaye. Wannan ya sanya tsoron lamarin zama yayi ko salo ga dimukuradiyyar Najeriya.