aAvengers na son mai shiga tsakani na waje
June 13, 2016Tsagerun yankin Neger Delta da suka yi kaurin suna wajen kai hare-haren a kan bututan man fetur a kudancin Najeriya sun bukaci kamfanoni kasashen waje masu zaman kansu da su amince da shiga tsakani a tattaunar sulhu da za su yi da gwamnati Najeriya.
A wata sanarwa da kungiyar ta wallafa a shafinta na Internet, Niger Delta Avengers,ta yi kira ga kamfanonin man da ke aikin hakar mai a kasar da su nemi hadin kan kamfanoni masu zaman kansu a kasahen ketare kan sun cimma yarjejeniyar zama teburin sulhu da gwamnati dan kawo karshen ayyukan fasa bututan mai a kasar.
A makon jiya ne dai kingiyar Niger Delta Avengers ta yi watsi da tayin da gwamnatin Najeriyar ta yi mata na sasantawa. Amma takwarata da ke zama kungiyar MEND da tayi fafutukar kafa yankin Biafra a baya ta ja kunnen sabbin tsagerun da su hau teburin sulhu da gwamnati.