1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsadar kudin sadaki na barazana ga Aure a Kamaru

Moki/ Aishat Bello Mahmud/ LMJMay 4, 2016

A yanzu haka wasu matasan kasar Kamaru sun fara hakura da batun aure, sakamakon abin da suka ce iyayen na dorawa masoyan yaransu mata nauyin biyan sadaki mai kauri.

https://p.dw.com/p/1IhlG
Tsadar aure na neman hana samarin kasar Kamaru yin sa
Tsadar aure na neman hana samarin kasar Kamaru yin saHoto: Getty Images/AFP/A. Joe

Biyan sadaki, da maza ke bayarwa kafin a kulla alaka ta auratayya dadaddiyar al'ada ce da ake gudanarwa a fadin Afrika da ma wasu sassan duniya, amma yanzu haka a Kamaru an fara watsi da al'adar ta biyan kudin aure ga dangi, duba da yadda sadakin matan ya yi tashin gauron zabi har ma ya fara gagarar mazan kasar. Wasu matasan kasar ta Kamaru dai a yanzu haka sun fara hakura da batun auren tare da koma wa gayin sadaka, sakamakon abin da suka ce iyayen yara mata na dorawa masoyan yaransu matan nauyin biyan sadaki mai kauri, baya ga karbar makudan kudade sai namiji ya bada shanu da awaki da aladu kowannen su 20 tare da katon din giya wanda shi ne yake a matsayin wata babbar kyautar da namiji zai bayar ta nuna alamun tabbatar da cewa ya zabi wannan budurwa a matsayin matarsa.

Amarya Marie Julienne yar kimanin shekara 22 dauke da murmushi tace Angonta ya biya sadakin aurenta kimanin dubu 16 na dalar Amurka, kana baa wai a nan batun ya tsaya ba.

Tace: "Banda wannan kudi ya kuma kawo buhun hunan shinkafa da albasa da Aladu haka kuma ya yiwa mahaifiyata da 'yan uwanta sutura haka ma mahaifina da 'yan uwansa. A cikin akwatunan da suka kawo sun saka kudi a ambulan wanda zan bawa dangina na kusa, ya kuma sayawa kannena maza keke yayin da 'yan uwana mata kuma ya saya musu keken dinki, A gidanmu ne aka yanke masa wadannan abubuwa da ya kawo."

Marie dai ta kammala jami'ar Douala, ta kuma ce iyayenta sun tambayi sadakin ne duba da kimar kudin da aka kashe mata wajen neman ilimi. Samarin garin Mimboman sun koka kan yadda kudin aure yake kara tashi, inda suka kai kokensu ga Reveran Poul Nimpa wanda jami'i ne a cocin katolika ya kuma fahimci matsalar ta matasan kasar na Kamaru. A cewar wani masanin halayyar dan Adam a kasar ta Kamaru Zogo Benjamin a lokuta da dama dai kudin sadaki na zarce kimar data dace na kulla danganta zuwa auren jari.