1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

IMF za ta bai wa Nijar da Burkina Faso rance

Ramatu Garba Baba
April 15, 2020

Asusun Lamuni na duniya zai taimaka wa kasashen Nijar da Burkina Faso da rancen kudi cikin gaggawa don su yaki annobar Coronavirus da ke ci gaba da yaduwa a wadannan kasashen.

https://p.dw.com/p/3ax4x
Washington The International Monetary Fund IMF | IWF Hauptquartier
Hoto: Reuters/Y. Gripas

A wannan Laraba Asusun bayar da Lamuni na duniya IMF, ya sanar da bayar da rancen gaggawa ga kasashen yankin Sahel da suka hada da Burkina Faso da jamhuriyyar Nijar, domin su yaki annobar Coronavirus da ke ci gaba da yaduwa a wadannan kasashen ba kakkautawa. Kasashen biyu za su sami rancen kudi na fiye da dala miliyan dari.


Hakazalika akwai wasu kasashe masu tasowa a yankin Afrika da za su ci gajiyar tallafin a yakar Coronavirus bayan da Asusun ya ce za a yafe wasu daga cikin basusukan da ake binsu domin karfafa musu gwiwa wajen fuskantar matsalar da ta zama ruwan dare gama duniya.