1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Angela Merkel ta lashe zaben Jamus

September 22, 2013

Jam'iyun CDU da CSU sun sami kyakkyawar nasara a zaben majalisar dokokin Jamus, wato Bundestag da aka gudanar ranar Lahadi

https://p.dw.com/p/19m40
Hoto: Reuters

Bayan kampe da neman kuri'un masu zabe na tsawon makonni da dama, ranar Lahadi a nan Jamus aka gudanar da zaben da shine afi muhimmanci a wannan shekara, wato zaben majalisar dokokin taraiya ta Bundestag, tare da yanke kudiri a game da mukamin shugaban gwamnatin Jamus nan gaba. Jim kadan bayan rufe runfunan zaben da karfe biyar daidai agogon Najriya aka sami abin da aka kwatanta a matsayin hasashen yadda sakamakon zai gudana, kafin daga baya a fara samun sakamako na hakika, daidai lokacin da ake kidaya kuri'un da aka kada. Sakamakon da ya samu ya zuwa yanzu, ya nuna cear jam'iyar CDU ta shugaban gwamnati Angla Merkel da abokiyar hadin gwiwarta wato CSU, gaba daya sun sami kashi arba'in da biyu da digo biyar cikin dari na kuri'un da aka kada. Hakan yana nufin shugaban gwamnati Merkel, ita ce zata fara samun damar neman kafa gwamnati. Sakamakon zaben ya baiwa wadannan jam'iyu biyu wato CDU da CSU karin fiye da kashi takwas cikin dari, idan aka kwatanta da shekaru hudu da suka wuce. Shugaban gwamnatin a lokacin da ta baiyana gaban dimbin magoya bayanta a Berlin, ta baiyana godiya ga masu zabe tare da cewa:

Nayi farin cikin wannan kyakkyawar nasara da amincewar da kuka bamu, kuma ina tabbatar maku da cewar ba zamu baku kunya ba. Zamu hada gwiwa tare daku domin tafiyar da aiyukan dake gabanmu nan da wasu shekaru hudu masu zuwa. Ko da shike tun a gobe zamu kafa kwamitin kwararru da zasu yi nazarin wannan aiki dake gabanmu, amma a yau, wajibi ne muyi biki.

To sai dai yar karamar jam'iyar dake kawance da CDU da CSU a tafiyar da gwamnatin taraiya, watu Free Democrats ko kuma FDP, ya zuwa yanzu babu alamun zata sake shiga majaisar dokokin ta Bundstag. Karkashin tsarin dokokin Jamus, duk jam'iyar dake son shiga majalisar dokokin taraiya ko majalisun jihohi ko na gundumomi a lokacin zabe, tilas sai ta sami akala kashi biyar cikin dari na yawan kuri'un da aka kada gaba daya. A yanzu jam'iyar ta FDP abin da ta samu bai wuce kashi hudu da digo shida cikin dari ba. Kakakin jam'iyar ta FDP dake sharhinsa na farko game da sakamakon zaben yace:

Duk irin sakamakon da ya samu a yammacin yau, wannan sakamako shine maafi muni a tarihin jam'iyar FDP tun daga shekara ta 1949. Da alamu bamu sami nasarar cika bukatun wadand suka zabe mu a cikin gwamnatin da ta gabata ba. Mun yi kokarin cika bukatun wadannan masu zabe ta hanyar manuifofinmu na tattalin arziki, amma bamu sami nasara ba, saboda haka zai zama wajibi jam'iyar ta FDP ta sake tsarin kanta.

Bundestagswahl Reaktion FDP Rainer Brüderle Philipp Rösler
Shugaban jam'iyar FDP Philipp Rösler(dama) da Rainr BrüderleHoto: Reuters

Wannan mummunan kaye da jam'iyar FDP tasha ya sanya jam'iyun CDU da CSU sun rasa abokiyar hadin gwiwa a taraiya, abin dake nufin idan har Angela Merkel tana son kafa sabuwar gwamnati bayan zaben na yau a taraiya, tilas kenan ta sami sabuwar jam'iyar da zata yi kawance da ita.

Ita kuwa jam'iyar adawa ta Social Democrats, wato SPD da ta shiga zaben tare da dan takara Peer Stinbruck da ya nemi mukamin shugaban gwamnati, ta sami kashi 26 ne cikin dari, kuma ita ce jam'iya ta biyu mafi girma bayan zaben na yau, tare da karin kashi uku cikin dari idan aka kwatanta da yawan kuri'un da ta samu a zaben shekara ta 2009. Shugaban jam'iyar ta SPD Sigmar Gabriel yayi wa magoya bayan jam'iyar sa jawabi kamar haka.

Mun sami kari a zabenn a bana, babu shakka, amma karin bai kai yadda muka sa rai ba. Tun da shike mu mutane ne da in kayardamu mun sani, saboda haka mun san cewar jam'iyar CDU CSU karkashin shugaban gwamnati Angela Merkel ta sami kyakkyawar nasara kuma daidi ne mu yi mata murna.

Bundestagswahl Reaktion SPD Steinbrück Steinmeier
Dan takarar jam'iyar SPD Peer Stinbrück(hagu) da Walter SteinmeierHoto: Reuters

Jam'iyar Greens ta sami kashi takwas cikin dari, abin da ya hadada koma bayan kashi biyu da digo shida cikin dari, sai jam'iyar masu neman canji, yayin da jam'iyar masu sukan manufofin nahiyar Turai, ko kuma AfD a takaice ta sami misalin kashi hudu da digo tara cikin dari.

Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita: Mohammad Nasiru Awal