Ana zargin tsohon fraiministan Indiya da badakalar cin hanci
March 11, 2015Talla
Wannan batu da ke zama mafi girman zargin cin hanci a kasar ta Indiya, wata babbar koma baya ce ga jam'iyyarsa ta Congress da tauraronta ke dada dusashewa.
Ana zargin gwamnatin wancan lokacin da sayar da wuraren hakar kwal masu yawa ba bisa ka'ida ba, da cin amanar kasa da kuma hadin baki don aiwatar da wasu munana ayyuka da ya janyo wa kasar asarar biliyoyin daloli, wadanda hukuncinsu zai iya zama daurin rai da rai. A lokacin dai Manmohan Singh shi ne ministan ma'aikatar hakar kwal a Indiya.
Sai dai kamfanin CBI, da ya gudanar da bincike kan batun, ya ce an gayyato tsohon primiyan ne kawai a matsayin wanda ake zargi. Tuni dai Mr Singh mai shekaru 82 da haihuwa ya musanta wannan zargi da ake masa.