1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Somaliya: Ana zargin tura sojoji Habasha

Abdul-raheem Hassan
January 27, 2021

Iyayen sojojin Somaliya na zargin gwamnati da tura 'ya'yansu yaki a arewacin yankin Tigray na Habasha a asirce, wannan batu dai ya fara daukar hankali ne bayan dena jin duriyar sojojin daga iyalansu.

https://p.dw.com/p/3oSyP
Somalia Tabda|  Kenianische Soldaten | Militäroffensive
Hoto: Ben Curtis/AP Photo/picture alliance

Matakin da ya kai ga 'yan majalisar dokoki rubuta wasika ta musamman na neman karin bayani ga Shugaban kasar Somaliya a madadin iyayen da suka zaku su san halin da yayansu ke ciki.

Gwamnatin Somaliyar dai ta musanta zargin tura sojojin kasar shiga yaki a Tigray, tare da cewa gwamnatin Habasha ba ta taba neman agajin sojojin daga Somaliya ba.