Ana zaman dar-dar tsakanin Indiya da Pakistan
January 8, 2013Hukumomin soji a kasar Indiya suka ce, an hallaka sojojinsu biyu, a wani musayar wuta da aka yi da wasu mutane dauke da makamai, a kan iyakar kasar da Pakistana, bangaren yankin Kashmir da ke samun takaddama tsakanin Pakistan da Indiya. Kakakin sojan Indiya a yankin yace, sojan kasar dake sintiri sun hangi gungun wasu mutane na kaikawo a kan iyakar ta su, bayan da sojan kasar suka nemi mutanen su yi surenda, sai kawai suka bude wa sojan wuta. Hatsarin yazo ne kwana biyu bayan da Pakistan tace soajan Indiya da suka getara kan iyakar da suke takaddama, sun hallaka sojan Pakistan daya. A wannan yankin da kasashen biyu da suka mallaki makamin nukiliya ke gardama a kansa, ana yawan samun hari kan juna, ko da yake yan shekarunnan dangantaka tsakanin kasashen biyu ta inganta. Gwamnatin Pakistan dai tuni ta musanta hannunta a harin da Indiya tace Pakistan ke da alhaki.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Mohammed Nasir Awal