'Yan Zambia na zaben shugaban kasa
August 12, 2021Talla
'Yan takara 16 ne dai ke fafatawa a zaben na wannan Alhamis, ko da yake ana ganin fafafatawar za ta fi zafi ne tsakanin Shugaba Edgar Lungu mai neman tazarce da abokokin hamayyarsa Hakainde Hichilema na jam'iyyar UPND.
Gabanin wannan ranar dai bangarorin biyu sun sha takun saka a cikin yanayi na gangamin yakin neman zabe mafi zafi da zargin juna musamman 'yan adawa da ke zargin Shugaba Lungu mai shekaru 64 a duniya da karya tattalin arzikin kasar. Wannan ne dai karo na shida da madugun adawa Hakainde Hichilema mai shekaru 59 ke takarar shugaban kasa.