Zaben shugaban kasa a Somaliya
May 15, 2022Adadin 'yan takara 36 ne ke takarar kujerar shuzagban kasa, ciki har da Shugaba Mohamed Abdullahi Mohamed mai ci a yanzu. Cikin 'yan takarar har da tsoffin shugabannin kasar guda biyu da kuma mace daya tilo da ke zama tsohuwar ministar harkokin wajen kasar. 'Yan takara biyu sun janye aniyarsu gabannin ranar zaben.
Manyan kalubale da ke jiran sabon shugaban kasar sun hada da dakile kungiyoyin ta'adda da tabbatar da hadin kan 'yan kasar da yaki da cin hanci da rashawa da kuma samar da yyuka musamman tsakanin matasa.
Duk da cewa kasar Somaliya ta fara shiga yakin basasa tun 1991, kasar na gudanar da zaben shugaban kasar duk bayan shekaru hudu tun a 2000, kodayake na baya-bayan nan an jinkirta shi tun 2021.
A cikin watan Fabrairu asusun bada lamuni na duniya IMF yayi gargadin hana kudin tallafi kusan dala miliyan 400 sai har an yi zaben ‘yan majalisa da na shugaban kasa wanda aka kammala a tsakiyar watan Mayun 2022.