1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana tunawa da shekara guda da harbo jirgin saman Malesiya

Suleiman BabayoJuly 17, 2015

Daukacin mutane kusan 300 da ke cikin jirgin saman Malesiya suka mutu lokacin da aka kakkabo jirgin a sararin samananiyar kasar Ukraine

https://p.dw.com/p/1G0lO
Ukraine Jahrestag Absturz MH17 Gedenken an Opfer in Kiew
Hoto: Reuters/G. Garanich

Kimanin mutane 200 a kauyukan gabashin kasar Ukraine sun halarci addu'oin alhinin tunawa da mutanen da suka rasa rayukansu a wajen da aka kakkabo jirgin saman kasar Malesiya shekara guda da ta gabata. Daukacin mutanen da ke cikin jirgin saman 298 sun hallaka, lokacin da wadanda ake zargin 'yan aware masu goyon bayan kasar Rasha suka kakkabo jirgin saman mai lambar tafiya MH17.

Galibin fasinjojin 'yan kasar Holland ne, kuma an gudanar da alhini a kasashen na Holland da Ostareliya gami da Malesiya. Shugaba Petro Poroshenko na Ukraine ya nemi ganin an kafa kotun Majalisar Dinkin Duniya domin hukuntan wadanda suke da hannu kan harbo jirgin saman na fasinja a sararin samaniyar kasarsa.