280212 Senegal Stichwahl
February 28, 2012Da alama dai shelar da shugaba Abdoulaye Wade na Senegal ya yi cewa zai sami nasara tun a zagaye na farko a zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar an yanka ta tashi domin shugaban ya kasa samun rinjaye da ya ksamata na lashe zaɓen kuma idan har haka ya tabbata to kam dole sai an kai ga yi zagaye na biyu na zaɓen a ranar 18 ga watan Maris inda za a sake karawa tsakanin shugaban mai barin gado da kuma Macky Sall.
A taron manema labaran da ya kira shugaba Abdoulaye Wade bai yi wata wata wajan cewar za a kai ga yin zagaye na biyu a zaɓen bayan da aka fara baiyana sakamakon wucin gadi na zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a ƙarshen mako.A ƙidayar da aka riga aka yi ta rabi ƙuri'un Wade ya sami sama da kashi 32 cikin ɗari na ƙuri'un da aka kaɗa yayin da Macky Sall ke da kashi 25 Ametrh Ndiaye malamin koyar da kimiyar Siyasa ne a Jami'ar Dakar.''ya ce ba wata tantama sai an kai ga yin zagaye na biyu a zaɓen shugaban ƙasar ya ce kuma abinda ke zama ma fi kyau kennan ga ƙasar domin kuwa kowa ya san cewar a ƙasar Senegal babu wani wanda ya isa ya lashe zaɓen shugaban ƙasa tun zagaye na farko.
Masu yin nazari akan al'amura na cewar zuwa zagaye na biyu shi ne mafi kyau
Kusan dukanin masu saka ido a zaɓen na ƙasahen duniya da na ƙungiyar Tarrayar Turai sun hallarci zaɓen wanda suke lura sau da kafa abubuwan da ke faruawa.Ko da shi a sahun jam'iyar yan adawa babu wani fargaba da ake da shi dangane da zagaye na biyu na zaɓen da ke ciki da rikici wanda tun da farko ƙawancen jam'iyyun adawar na M23 suka so hana shugaba Aboulaye Wade tsaya wa takara saboda hujar cewa ya saɓama kudin tsarin mulki. To sai dai jam'iyyar da ke yin mulki ta PDS ta ce komai na iya faruwa domin za ta iya ƙula ƙawance da ya dace domin samin nasara a zagaye na biyu abinda ake gani zai iya sa a kai ga shawo kan wasu yan adawar domin canza sheƙa Babacar Gaye na jam'iyyar ta PDS ya ce su na sa ran samin nasara ta ko wane hali.''ya ce duk masu neman ganin ƙasar Senegal ta cimma kyaukyawar makoma ya ce to kam zasu kaɗa ma shugaba Wade ƙuri'a kuma ya ce ba tabas ba nE dukanin sauran yan siyasar na adwawa su ƙi kadama Wade ƙuri'a.
A kwai fargaba kada wasu yan adwa su koma goyon bayan shugaba Abdoulaye Wade
Za a yi cewa dai yanzu ta ke dangane da rawar da yan siyasar sukan iya taka wa ta ƙwace mulki ta hanyar dimokaradiyya daga hanun mutunin da ya so ya yi tazarce.kuma masu lura da al amura na hasashen cewa Macky Sall jagoran jam'iyar APR Alliance Pour la Republique tilas ne ya dage ga ƙara neman goyan bayan sauran yan siyasar:Abdoulaye Wilane jigo ne na jam'iyyar yan gurguzu ɗaya daga cikin jam'iyyun siyasar na M23. ''ya ce har yanzu babu wata shawara da muka tsaida mu ƙawance mai haƙida ya ce muna da buri ba yan a bi yarima ba ne a sha kiɗa ya ce muna mutunta masu kaɗa mana kuri'a ya duk shsawara da zamu yanke zata kasance ta bai ɗaya tare da yarjejeniya a cikin kawancen. Kawo yanzu dai wasu yan takara ba su baiyana matsayin su ba in ba Moustapha Niasse ba wanda ya ce shi babu wata shawar da zai iya yanke wa sai abinda ƙawance yan adawar ya tsayar ko mi ta ke zama dai sai na gaba a ranar juma'a mai zuwa loakacin da za a baiyana sakamakon a hukumce a lokacin za a fara sannin matsayin yan siyasar.
Daga kasa za a iya sauren wannan rahoto
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman