1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ganin bakin jinin Jamus game da rikicin kudin Euro

March 22, 2013

Jamus ke ba da kaso mafi yawa a asusun tallafa wa kasashen tarayyar Turai dake fama da matsalolin tattalin arziki, amma duk da haka tana shan suka.

https://p.dw.com/p/182tL
GettyImages 164058650 Cypriot protestors wave banners picturing German Chancellor Angela Merkel (C) and Cypriot President Nicos Anastasiades (R) during a demonstration against an EU bailout deal outside the parliament in the capital, Nicosia, on March 19, 2013. The speaker of the Cypriot parliament urged MPs to say 'no to blackmail' in a vote on a eurozone bailout aimed at saving the Mediterranean island from bankruptcy. AFP PHOTO/BARBARA LABORDE (Photo credit should read BARBARA LABORDE/AFP/Getty Images)
Hoto: AFP/Getty Images

Tarayyar Jamus musamman shugabar gwamnati Angela Merkel na shan suka da kakkausan lafazi a kasashen Turai dake fama da rikicin kudi, saboda tsauraran matakan farfado da tattalin arziki da Jamus din ke kira da a dauka.

Shugabar gwamnatin ta Jamus ba za ta iya kallon hotunan da aka zana ta a cikin kayan 'yan Nazi ko da gashin bakin Hitler ba. Tun farkon rikicin kudi a kasashe masu amfani da kudin Euro, masu adawa ke sukar Jamus da abin da suka kira matakan tsimi da kasar ke matsa kaimi da a dauka, inda ma suke yawaita kwatanta Jamus da lokacin 'yan Nazi.

Hatta yanzu ma a Cyprus, inda dubban masu zanga zanga a gaban majalisar dokokin kasar ke rike da alluna na adawa da kuma batanci ga Merkel da Jamus.

epa03425966 A demonstrator holds a poster depicting Adolf Hitler and German Chancellor Angela Merkel during a protest in front of the Parliament building against new austerity measures in Athens, Greece, 08 October 2012. The protest, called by trade unions, took place one day ahead the visit of German Chancellor Angela Merkel in Athens. The banner reads 'Dont buy German products, Resistance against fourth Reich'. EPA/ORESTIS PANAGIOTOU +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture-alliance/dpa

Jamus na shan suka game da rikicin kudin Euro

Da yawa daga cikin 'yan Cyprus sun dora wa Jamus laifin tsauraran sharuddan da tarayyar Turai ta gindaya wa kasar na ceto tattalin arzikinta. Ga 'yan siyasar kasar, Merkel da ministan kudin Jamus Wolfgang Schäuble suka matsa lamba na ganin an dauki wadannan matakan dora wani nauyi a kan masu ajiyar kudi a Cyprus. Sai dai Andreas Armenakis na wata kungiyar karfafa hulda tsakanin Jamus da Cyprus ya ce ba dukkan 'yan kasar ne ke da irin wannan tunani ba.

"Ba na jin daukacin al'umar Cyprus na ganin bakin jinin Jamus. Kamar a zanga-zangar baya nan, akasarin rubuce rubucen da aka yi kan allunan masu zanga-zangar sun yi tir da ne da bankuna, kalilan ne a cikinsu suka soki lamirin shugabar gwamnatin Jamus."

Sai dai gwamnati a birnin Berlin na da ra'ayin daban game da rabon rawar da kowace za ta taka. Gwamnatin Cyprus ta ki amince wa da sanya haraji mai yawa ga masu ajiya da yawa a bankuna. A saboda haka masu kokarin ceto kudin Euro sun kasa samun wata maslaha da al'uma za ta iya dauka. 'Yan Cyprus dai inji Andreas Armenakis na ganin tamkar cin mutunci ne inda aka zarge su da haramta kudin haramu.

"Idan kura talafa ba wanda zai sake yin irin wannan tunani. A gani na 'yan Cyprus ba za su dauki lokaci mai tsawo suna ganin bakin jinin Jamus ba. Sannu a hankali za su fahimci halin da ake ciki, kuma da zarar an magance matsalar komai zai lafa."

A zanga-zangar kin amincewa da matakan tsimi a kasar Girika ma shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta sha tofin Allah tsine. A kasar ta Girika an dade ana nuna fargaba game da wani babakere daga Jamus, musamman ta la'akari da ta'asar da sojojin Jamus suka aikata a lokacin yakin duniya na biyu.

Kin jinin Jamus ba yawa a kasar Spaniya

A Italiya ma Jamus ta sha kakkausan suka a watannin baya dangane da batun na rikicin kudin Euro. Sai dai a kasar Spaniya sabanin Girika da Italiya sukar da aka yi wa Jamus ba yawa, inji Fernando Vallespin masanin kimiyyar siyasa a jami'ar birnin Madrid.

Das Titelblatt der italienischen Zeitung «Il Giornale» vom 03.08.2012 aufgenommen in Castel Gandolfo. Das Blatt aus dem Medienimperium von Silvio Berlusconi hat die Äußerungen von EZB-Chef Mario Draghi zur Rettung des Euro kommentiert. «Heil Angela», heißt es auf der Titelseite unter einem Foto, das die Kanzlerin zeigt, wie sie die rechte Hand hebt. Foto: Karl-Josef Hildenbrand dpa/lby +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture-alliance/dpa

"Abin mamaki shi ne a kasar Spaniya ba a ganin bakin jinin Jamus ba. A kullum ana yi wa Jamusawa kallon kawayen mu. Abin da ake gani yanzu ba adawa ce ga Jamus ba, adawa ce da manufar tsuke bakin aljihun gwamnati, wato matsala ce da gwamnati amma ba Jamus ba."

A halin yanzu dai gwamnati a Berlin ta gane irin bakin jinin da take da shi a kasashen kudancin Turai, a saboda haka ta fara wani kamfe na wanke kanta a wasu kasashen kamar irin su Girika.

Mawallafa: Nils Naumann / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Mohammad Nasiru Awal