1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana cikin rudani a fadar shugaban kasar Nijar

July 26, 2023

Kawo yanzu ba tabbas kan halin da Shugaba Mohamed Bazoum na Nijar yake ciki, bayan da sojoji suka garkame fadar shugaban kasa tare da gidansa.

https://p.dw.com/p/4UPjh
Deutschland l Besuch des Nigerianischen Präsidenten in Berlin
Hoto: Presse- und Kommunikationsdienst der Präsidentschaft von Niger

Kungiyar raya tattalin arzikin Afirka ta Yamma ECOWAS, ta yi Allah wadai da abin da ta kira yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Nijar.

Da safiyar yau Laraba ne dai sojojin da ke tsaron fadar Shugaba Mohamed Bazoum, suka garkame ko'ina tare da tsare shugaban kasar.

ECOWAS dai ta yi kiran sojojin da su gaggauta sakin sakin zababben shugaban gwamnatin farar hula a Nijar din.

Kungiyar ta kuma ce da ita da kasashen duniya, za su hukunta duk wadanda alhakin kare lafiyar Shugaba Bazoum da iyalansa da sauran jami'an gwamnatin kasar ke a hannunsu.

Majiyoyi daga fadar Shugaba Bazoum dai sun ce hatta sauran ma'aikata da ke aiki a ofishi ba a kyale su domin shiga harabar ba a yau.

Kungiyar Tarayyar Afirka ma ta yi tir da abin da sojojin suka yi a Nijar, inda shugabanta Moussa Faki Mahamat ya yi kiran da su janye matakinsu.

Matakin sojojin na Nijar ya zo daidai da wanda sojojin juyin mulki suka dauka a kasashen da ke makwabtaka da kasar irin su Mali da Burkina Faso.

Kasar ta yi kaurin suna ta fuskar gamuwa da juyin mulki tun bayan samun ‚‘yanci daga Faransa a shekarar 1960.

Juyin mulki na karshe a Nijar dai shi ne wanda sojojin suka yi wa gwamnatin tsohon Mamadou Tandja.