Ana cikin fargaba na lalubo masu hakar zinare a Najeriya
June 8, 2024Hukumomi sun bayyana cewa mutum daya ya rasa ransa a yayinda aka yi nasarar kubutar mutum shida dauke da munanan raunuka, a hadarin da ya rutsa da masu hakar zinaren a ranar litinin din da ya gabata.
Karin bayani: Kasa ta rufta da mahaka tagulla a Zambiya
Mai magana da yawun hukumar bada agajin gaggawa a jihar Niger Ibrahim Audu Husseini, ya ce sun gamu da cikas wajen gudanar da aikin ceton ba kamar yadda sukayi hasashe ba. Ya ce sakamakon girman matsalar a yanzu haka ma'aikatan hukumar na amfani da shebura da sauran kayan aiki na gargajiya wajen nemo mutanen da suka makale sakamakon karancin kayan aiki na zamani da hukumar ta SEMA ke fama da su.
Karin bayani: An sace 'yan China a mahakar ma'adinai a Najeriya
A ranar larabar da ta gabata jami'an 'yan sanda sun ce mutane 20 ne suka makale, inda hakan ya kore alkaluman farko da hukumar agajin gaggawa ta Najeriyar ta fitar, na cewa masu hakar zinaren sun haura mutum 30 a karkashin kasa.