1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An zargi sojojin Najeriya da cin zafin jama'ar Maiduguri

July 26, 2011

Ƙungiyoyin kare yancin bil'adama sun zargi sojojin da aka tura birnin Maidugurin Najeriya da cewa suna ci zarafin fararen hula. Inda suke yin sata da kisan mutane da yi wa mata fyaɗe, sai dai gwamnatin ta musanta

https://p.dw.com/p/124cY
Kasuwar MaiduguriHoto: Katrin Gänsler

A wani abun da ke zaman kokarin su na kaucewa cigaban fuskantar suka game da rawar da jami'an tsaron Najeriya ke takawa a birnin Maiduguri, gwamnatin kasar tace zata kaddamar da bincike kan jerin zarge-zargen take hakkin bil'adamar da ke kara karfi a tsakanin kungiyoyin kare hakkin bil'adama a ciki dama wajen kasar ta Najeriya.

Parlamentswahl in Lagos Nigeria
'Yan sandan NajeriyaHoto: DW/Thomas Moesch

Duk da cewar dai an dauki tsawon lokaci ana musayar yawu a tsakanin mazauna birnin na Maiduguri dake zargin rundunar tsaron kasar da cin zarafi dama kisan ba gaira da kuma rundunar da tace karatun na yan Maiduguri na zaman karatun kura, matsayi ya sauya a yayin da kungiyar Amnesty International mai fafutukar kare hakkin bil'adama ta fito ta tabbatar da asarar rayuka dai dai har 23 a wani fito na fiton da aka yi tsakanin sojan da kuma mazauna Anguwar Budun a birnin na Maiduguri a karshen mako.

Abun da kuma yanzu haka ke kara tada hankula a tsakanin al'umar ta Maiduguri dama kungiyoyin da ke wa kisan kallo irin na ba gaira da kuma suka gargadi gwamnatin kasar da ta kawo karshen kisan da sojan ke yi a birnin.

Martanin gwamnati

Nigerias Präsident Goodluck Jonathan
Shugaba Jonathan da mataimakinsa SamboHoto: AP

To sai dai kuma gwamnatin da ta ke maida martini kan sabbabin kashe-kashen dama kona kasuwar da ake zargin sojan da yi dai, tace za ta kaddamar da bincike domin abun da ministan tsaron kasar Dakta Bello Halliru Mohammed ya kira tabbatar da ko sojan sun karya ka'idojin aikin da aka basu.

Kisan da ke zaman irin sa mafi yawa a lokaci guda dai na zaman na baya baya cikin jerin kashe-kashen ba gaira da ake zargin sojan da yi kan fararen hula a birnin na Maiduguri.

Neman a janye sojoji

Ko a farkon wannan wata da muke ciki dai dattawan birnin sun nemi gwamnatin da ta janye sojan bayan da aka rika samun karuwar rahottanin cin zarafin al'ummar ta Maiduguri da suka hada da fyaden mata da cin mutuncin yara kanana.

Duk da cewa dai gwamnatin ta dage kan sojan na da rawar takawa a kokarin kawo karshen rikicin da ya lamushe rayuka kusan 200 a cikin kasa da tsawon wattani bakwai da suka gabata dai, harin na iya kara matsa lamba ga gwamnatin da a baya ta yi alkawarin sulhu tsakanin ta da 'ya'yan kungiyar ta Boko Haramun.

Kashim Shettima, Gouverneur von Borno State, Nigeria
Kashim Shettima gwamnan jahar BornoHoto: DW

Matakin da gwamnati ta dauka

Tuni dai gwamnatin ta fara karkata ya zuwa wani sabon kamfen din janyo mazaunan na Maiduguri cikin shirin kawo karshen aiyukan 'ya'yan kungiyar da ke neman gagarar sarki da ma talaka a kasar ta Najeriya.

Kamfen din kuma da cewar Dakta Hallirun ya kunshi sake dora aminci da abota da jami'an tsaron.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Ahmadu Tijjani Lawal