An zargi Jammeh da kisan 'yan Afirka
May 16, 2018Kungiyoyin Human Right Watch da TRIAL da ke kare hakkin dan Adam a duniya sun zargi tsohon shugaban kasar Gambiya Yahya Jammeh da ba da umurnin kisan wasu 'yan gudun hijira kimanin 50 daga kasashen Ghana da wasu kasashen Afirka ta Yamma a loakcin da yake kan kujerar mulki a kasarsa.
A cikin wata sanarwar hadin gwiwa da wadannan kungiyoyi biyu suka fitar a wannan Laraba, sun bayyana cewa lamarin ya wakana ne a watan Yulin 2005 a bakin wata gabar ruwan kasar ta Gambiya kusa da birnin Banjul da kuma kan iyaka da kasar Senegal, inda jami'an tsaro na wata rinduna ta musamman ta shugaba Jammeh, suka kama wasu 'yan gudun hijira 'yan kasar Ghana su 44 da wasu saura daga kasashen Najeriya da Senegal da Togo da ke hankoran zuwa Turai, kana suka bindige su a bisa zargin kasancewa sojojin haya da aka dauko domin kifar da gwamnatinsa.
Kungiyoyin na Human Right Watch da TRIAL sun ce sun samu wadannan bayanai ne daga bakin wasu tsaffin shugabannin sojin kasar ta Gambiya.