An yi husufin rana a kasashen duniya da dama
September 1, 2016Talla
Husufin dai makamancin wanda ake samu ne duk shekara, wanda ke faruwa idan duniyar wata ta gifta gaban rana. Husufin ya baiyana sosai a da'irar Afirka ta Yamma daga Gabon zuwa Kwango ya kuma dangana zuwa arewacin Mozambik..
Haka nan kuma husufin na rana ya baiyana sama-sama a sauran yankuna da suka hada da Tanzaniya da Madagaska. Mutane da dama wadanda ba su da masaniya game da aukuwar husufin sun yi mamakin yadda cikin kankanin lokaci yanayin rana a sararin samaniya ya sauya ya yi duhu.
Husufin dai ya dauki 'yan mintoci uku ne kacal. A kan sami husufin rana a bayan duk watanni goma sha takwas.