Rushewar ginin makaranta ya kashe mutane a Jos
July 12, 2024Talla
Rahotanni daga Najeriya na cewa, gawarwaki da dama ne aka samu a karkashin baraguzan makarantar da ta ruguje a jihar Filato da ke tsakiyar kasar a wannan Juma'a.
Ginin mai hawa biyu, mallakar Saint Academy da ke unguwar Busa Buji cikin gunduwar Jos ta arewa, ya rushe ne a lokacin makaranta da misalin karfe 07:30 agogon GMT, wanda ya sanya damuwa kan halin da dalibai da malamai ke ciki.
Ya zuwa yanzu dai an ceto dalibai biyar da ransu., a yayin da ake cigaba da aikin ceto tare da jami'an tsaro ciki har da sojoji da 'yan sanda a wurin.