An yaba wa hukunci ICC kan Ratko Mladic
November 23, 2017
Da yake tsokaci kan wanann hukunci wanda kotun ta yanke a jiya Laraba, babban kwamishinan kare hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya Zeid Ra'ad al Hussein wanda ya bayyana Ratko Mladic a matsayin tushen zalunci, ya ce wannan hukunci na a matsayin wani kashedi ne ga duk wasu azzaluman duniya:
"Wannan hukunci wani hannunka mai sanda ne ga duk wasu masu aikata laifukan yaki na su fahimci cewa duk irin karfin ikon da suke takama da shi ko badan-badade za su kare a hannun shari'a."
Kungiyar Tarayyar Turai da ma kasar Amirka sun yi kira ga kasashe da al'ummomin yankin balkan da su yi aiki kafada da kafada domin gina makomarsu a tare.
Kotu dai ta samu Ratko Mladic dan shekaru 74 a duniya da aikata laifuka guda 10 da suka hada da kisan kiyashin da aka aikata a Srebrenica na tsohuwar kasar Yugoslaviya, inda sojoji suka hallaka Musulmi dubu takwas a shekara ta 1995.