1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaKenya

An tuhumi malamin addini a Kenya da ta'addanci

July 8, 2024

Da ranar Litinin ne aka saurari tuhumar ta'addanci da ake yi wa wani malamin addinin Kirista na kasar Kenya, wanda ya yi sanadin mutuwar sama da mabiyansa mutum 440 cikin watan Afrilun bara.

https://p.dw.com/p/4i1yw
Fasto Paul Mackenzie a zaune a kotu
Fasto Paul Mackenzie a zaune a kotu da ke Mombasa na kasar KenyaHoto: Halima Gongo/DW

Mutumin da ya bayyana kansa a matsayin Pastor Paul Mackenzie, ya gurfana ne a wata kotun da ke birnin Mombasa, inda a bara Pastor Mackenzie ya ceda mabiyansa suna iya daina cin abinci har su mutu, domin zuwa su hadu da Yesu Kirista.

Malamin addinin na Kirista wanda ke da 'ya'ya bakwai da wasu abokan aikinsa mutum 90, ya musanta zargin aikata kisan kai da aka yi masa a kotu cikin watan Janairu.

Hukumomi a Kenya dai sun tilasta tono gawarwakin mutanen da suka mutu, domin binicke kan batun da ya yi matukar daukar hankalin duniya a baran.