Martani a kan tsawaita wa'adin karbar tsoffin kudi
January 29, 2023Gwamnan babban bankin Najeriyar Godwin Emefiele ne ya sanar da wannan karin a wata sanarwa da ya rattaba wa hannu a Lahadin nan (29.01.2023) a Abuja, inda ya yi bayanin cewa an kara wa'adin maida tsofaffin kudadden farawa daga ranar 1 ga watan Febriaru zuwa 10 ga wata.
Dama an tsara cewa za'a dakatar da amfani da kuma karbar tsofaffin kudin ne daga ranar 31 ga watan nan. Sanin cewa harkokin kasuwanci sun kama hanyar tsayawa cik, ko wane amfani wannan kari zai yi ga tattalin arzikin Najeriyar? Mallam Yusha'u Aliyu Masanin harkokin tattalin arziki ne da ke Abuja, da ke da ra'ayin cewar wannan mataki zai taimakaw mutane samun lokaci na mayar da tsoffin kudaden na su zuwa banki.
Mallam Isa Abdulmumini daya daga cikin jami'an sashin yada labaru na babban bankin Najeriyar ya tabbatar man da wannan Karin wa'adi. Karin lokaci na nuna bada kai da gwamnatin ta yi saboda matsin lamba da ta fuskanta kama daga shugabannin addininai ‘yan siyasa da na al'umma.
Ga ‘yan Najeriya musamman masu karamin karfi kamar yau take Sallah musamman masu sana'ar aikewa da kudi da aka fi sani da POS ko kuwa kun fi banki.
Babban bankin Najeriya ya ce sauya kudin ya sanya samun nasarar maido da kudi a bankuna. A shekara ta 2015 kaso daya daga cikin hudu ne na kudade ke hannun jama'a yayin da bilyan 500 kadai ke a bankuna, a 2022 wannan ya karu zuwa tirliyan 3.23. A yanzu an samu maido da kashi 75 na wannan adadi.