1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsatsaurar matakai a kan corona a Jamus

Abdourahamane Hassane
February 11, 2021

Gwamnatin Jamus ta tsawaita dokar kulle saboda corona har ya zuwa ranar bakwai ga watan Maris

https://p.dw.com/p/3pDxu
Deutschland Coronavirus Angela Merkel Bundestag
Hoto: Bernd von Jutrczenka/dpa/picture-alliance

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi gargadin cewar sai an yi juriya a kokarin da ake yi na yakar annobar corona. Wannan furci na  Merkel ya biyo matakin da gwamnatin ta Jamus ta dauka na tsawaita dokar kulle har ya zuwa ranar bakwai ga watan Maris. Sakamakon yadda kwayoyin cutar na corona mai rikida ke kara bazuwa a Turai wadanda ke zaman hadari ga rayuwar dan Adam amma duk da haka jama'a na adawa da matakin. A karkashin dokar ta kule za a ci gaba da rufe gidajen cin abici da na shayi da kantuna da shaguna da gidajen tarihi. Sai dai Merkel ta ce za a sake bude makarantu da shagunan gyaran gashi a ranar daya ga watan Maris, amma sai sun kasance cikin kyakyawan matakan riga kafi.