An tafi Charles Taylor zuwa Saliyo
March 29, 2006Talla
Tsohon shugaban kasar liberia charles Taylor ya isa kasar sa a yau laraba,inda dakarun Majalisar Dinkin Duniya suke dakonsa a filin jirgin saman birnin Monrovia inda ya sauka.
Kanfanin dillancin labarai na Reuters ya bada rahoton cewa,Jamian Majalisar Dinkin Duniya dauke da makamai suka wuce da taylor cikin wani jirgi mai saukar angulu na majalisar zuwa saliyo.