SiyasaAfirka
An dage zaben Somaliya
February 6, 2021Talla
An dakatar da gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalissu da aka shirya gudanarwa ranar Litinin mai zuwa a Somaliya.
Soke zaben da aka yi a wannan Asabar zai bai wa Shugaba Mohamed Abdullahi Farmajo damar ci gaba da jan ragamar mulkin kasar duk kuwa da cewa sauran kwanaki 6 kachal wa'adin mulkinsa ya kawo karshe.
Dama dai Farmajon na cikin jerin 'yan takara da ke zawarcin kujerar shugaban kasar na wani wa'adin shekaru 4 nan gaba.
An shirya gudanar da babban zaben kasar ne a ranar Litinin mai zuwa 8 ga wata Febrairu. Sai dai Somaliya ta kwashe shekaru sama da 30 ba ta gudanar da zabe gama gari ba, inda wasu kwamintin amintattu mai mutane 51 ne ke zaben shugaban kasa.