An yi watsi da takardun takarar dan tsohon shugaban Libiya
November 25, 2021A wannan Laraba da ta gabata hukumar zaben kasar Libiya ta soke takarar Seif al-Islam Gaddafi dan tsohon shugaban kasar Marigayi Moammar Gaddafi, daga cikin 'yan takara da ke neman shugabancin kasar a zaben da aka tsara na watan gobe na Disamba.
Hukumar zaben ta ce ta dauki wannan mataki saboda ya fusakanci hukuncin da aka daure shi a kasar. A shekara ta 2015 wata kotu da ke birnin Tripoli fadar gwamnatin kasar ta yanke hukuncin kisa ga Seif al-Islam Gaddafi saboda amfani da karfi kan masu zanga-zangar juyin-juya hali na shekara ta 2011 lamarin da ya kawo karshen gwamnatin mahaifinsa Marigayi Moammar Gaddafi ta fiye da shekaru 40. Sai dai an yi masa ahuwa a shekara ta 2017, amma har yanzu kotun duniya mai hukunta manyan laifuka yaki tana neman Seif al-Islam Gaddafi ruwa a jallo.
An tsara zaben shugaban kasar zagaye na farko ranar 24 ga watan gobe na Disamba a kasar ta Libiya da ke yankin arewacin Afirka, sakamakon kwarya-kwaryar zaman lafiya bayan kulla yarjejeniya tsakanin kungiyoyin masu hamayya da juna.