1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sanar da da sabon shugaban kasa a Aljeriya

Binta Aliyu Zurmi
December 13, 2019

Hukumar zaben kasar Aljeriya ta sanar da tsohon Firaministan kasar Abdelmajid Tebboune a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar.

https://p.dw.com/p/3UlhL
Algerien Abdelmadjid Tebboune Wahlsieger Präsidentschaftswahl
Hoto: picture-alliance/AP/F. Guidoum

Abdelmajid Tebboune ya lashe zaben ne da kaso 58 cikin 100 na kuri'un da aka kada kamar yadda shugaban hukumar zaben kasar Mohammed Sharafi ya bayyana.

An gudanar da babban zaben ne watanni takwas bayan wata zanga-zangar da ta yi sanadiyar faduwar gwamnatin tsohon shugaban kasar Abdelaziz Boutaflika. 
 
Sakamakon zaben dai na fita daidai loakcin da ake sa ran fitowar daruruwan al'ummar kasar don gudanar da zanga-zanga a wani mataki na nuna adawa da zaben da ma wadanda suka yi takara ta zama shugaban kasar na gaba.