An samu tsaiko a sasanta rikicin Libiya
January 14, 2020Da fari dai ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov ya ce kusan dukkanin masu jayayya da juna a rikicin kasar Libiya, sun sanya hannu kan yarjejeniyar ta tsagaita buda wuta, in banda madugun yakin Libiya Khalifa Haftar da kakakin daya bangaren majalisar dokokin Libiyar Aguila Saleh. Sai dai a karshe Khalifa Haftar ya fice daga kasar ta Rasha ba tare da ya sanya hannun ba, duk da sanarwar da Mr. Lavrov ya bayar na yiwuwar mutanen su sanya hannu kan yarjejniyar da safiyar Talata.
Madugun yakin na Libiya ya bukaci cimma wata bukata ce da ta shafi hannun Hadaddiyar Daular Larabawa. Sakataren harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov, ya ce za dai a cimma matsaya kan wannan batu. Nan gaba cikin wannan watan na Janairu ne dai ake sa ran bangarorin masu jayayya da juna za su sake wani zaman a Berlin fadar gwamnatin Jamus.