An samu karancin allurar riga-kafin sankarau a Najeriya
March 30, 2017Talla
Najeriya na fuskantar karancin allurar riga-kafin cutar sankarau da ta yi sanadiyyar rayukan akalla mutane 280 tun barkewarta a cikin watan Nuwamban 2016, inji manyan jami'an kiwon lafiyar kasar. Shugaban cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa a Najeriya, Chikwe Ihekweazu ya ce kawo yanzu sun yi rajistar mutane kusan 2000 a fadin kasar da ake zaton sun kamu da cutar amma 109 kawai aka tabbatar, tun bayan rahoton farko a jihar Zamfara.
Jihohin Zamfara da Sakkwato da Katsina da Kebbi da kuma Neja su ne suka fi fama da cutar a wannan karon. Wani jami'in cibiyar ya bayyana karancin allurar da cewa babban lamari ne.