An samar da yarjejeniyar tsagaita wuta a Lebanon
November 27, 2024Daruruwan al'umma da suka tsere daga gidajensu a kudancin Lebanon sun fara komawa gida jim kadan bayan fara aiki da yarjejeniyar a tsakanin Isra'ila da mayakan Hezbollah.
Wannan yarjejeniyar ta maido da zaman lafiya a Lebanon tuni ta saka fatan dakile yiwuwar bazuwar rikici a yankin Gabas ta Tsakiya, wanda ake fatan za ta share fagen samar da yarjejeniya ta din-din-din a Lebanon da ma Gaza.
A ranar Talata ce bangarorin biyu suka amince da kawo karshen zubar da jinin fararen hula, wanda ko a safiyar ranar sama da mutane 40 ne wani harin Isra'ila ya hallaka, wanda mayakan Hezbollah daga nasu bangaren suka harba rokoki zuwa arewacin Isra'ila.
Tuni shugabannin kasashen duniya irinsu Joe Biden na Amurka da na Emmanuel Macron Faransa suka yi murna da wannan mataki.