An sallamo wasu 'yan kasashen waje da aka sace a Najeriya
February 25, 2016Talla
Wannan labari ya fito a wannan Alhamis daga wani kamfani da ke ba da shawarwari kan harkokin tsaro na kan ruwa, da kuma ofishin harkokin wajen kasar Rasha. A ranar 29 ga watan Janairu ne dai maharan suka kame mutanen da suka hada da 'yan kasar Philippins biyu, 'yan kasar Rasha biyu da kuma dan kasar Georgiya daya.
Sai dai da yake magana kan batun sakin wadanda aka yi garkuwan da su, Dirk Steffen wani masani kan harkokin fashin teku ya tabbatar cewar an sako mutanen ne tun a ranar Asabar, sai dai bai bayyana yadda aka yi aka sallamo sun ba.