1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sake tono gawarwakin 'ya'yan Mandela

July 3, 2013

Shekaru biyu da suka gabata ne jikansa Mandla Mandela, ya kaurar da gawarwakin daga kauyen Qunu da Mandela ya girma zuwa mahaifarsa dake Mvezo.

https://p.dw.com/p/191lA
Former South African President Nelson Mandela's daughter Makaziwe Mandela (L) and grandson Ndaba Mandela (C) prepare to leave at the end of a court case concerning the removal of the remains of three of the ailing anti-apartheid hero's children, in the High Court of Mthatha in the Eastern Cape of South Africa July 2, 2013. Sixteen members of the Mandela family have already won a court order forcing Nelson Mandela's grandson Mandla Mandela - officially chief of the Mandela clan - to return the bodies that he dug up two years ago from the village of Qunu, where Nelson Mandela grew up. REUTERS/Siegfried Modola (SOUTH AFRICA - Tags: POLITICS)
Hoto: Reuters

A yau ne aka tono gawarwakin 'ya'yan Nelson Mandela guda uku, domin sake binnesu a kauyen Qunu inda Mandela ya girma. A wannan larabar ce dai Alkalin wata kotu a kasar Afrika ta kudu, ya umurci jikan Nelson Mandela, da ya tono gawarwakin 'ya'yan shugaban gwagwarmayar launin fatar guda uku, domin mayar da su asalin inda kaburrukansu suke. Wannan dai shi ne takaddamar baya-bayannan da ya raba kawuwan iyalan na Mandela da a yanzu haka yake matsanancin hali na jinya a asibitin Pretoria. Alkali kotun yanki a Mthatha, Lusindiso Pakade, ya bukaci Mandla Mandela mai shekaru 39 da haihuwa, wanda kuma shi ne shugaban zuri'ar Mandela a hukumance, da ya daraja wa umurnin na Kotu. Tun shekaru biyu da suka gabata ne dai Mandla ya mayar da gawarwakin zuwa kauyen Mvezo mai tazarar km 20 daga gabashin Cape, inda kuma aka haifi Nelson Mandela.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Mouhamadou Auwal Balarabe