An sake kwantar da Mandela a asibiti
June 8, 2013Talla
Fadar gwamnatin kasar ta Afrika ta Kudu ta ce da gabannin wayewar garin yau ne aka rugu da Mandela asibiti bayan da jikinsa ya yi tsanani.
Mahukuntan na Afrika ta Kudu dai sun ce Mandela na cikin wani hali sai dai likitoci na nan su na ta kokarin shawo kan wannan matsala da tsohon shugaban dan shekaru casa'in da hudu da haihuwa ke fuskanta a halin yanzu.
Wannan dai shi ne karo na biyu da aka kwantar da dattijon a asbiti cikin makonni takwas din da su ka gabata kan wannan matsala.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Usman Shehu Usman