An sake cafke Kabiru Sokoto
February 10, 2012Hukumomin tsaro a Najeriya sun ce sun sake cafke Kabiru Sokoto mutumin da ake zargi da kasancewa kan gaba wajen kai mummunan harin Bam na ranar Kirsimeti a garin Madalla wanda ya kuɓuce a hannun 'yan sanda ya tsere a watan da ya gabata. 'Yan sandan sun ce sun yi nasarar sake cafke Kabiru Sokoto ne yau Juma'a a wata 'yar Bukka a garin Mutum biyu a gabashin jihar Taraba da ke kan iyaka da ƙasar Chadi. Hukumar leƙen asiri ta SSS ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa a yanzu haka an tafi da Kabiru Sokoton zuwa Abuja. A ranar 18 ga watan janairun da ya gabata ne Kabiru Sokoto ya tsere daga hannun 'yan sanda a wani yanayi da hukumomin tsaro suka baiyana da cewa mai ɗaure kai, lamarin kuma da ya kai ga shugaban ƙasar Goodluck Jonathan ya kori sufeton 'yan sandan ƙasar Hafizu Ringim da mataimakansa su shida. Ƙungiyar Boko Haram ta ayyana ɗaukar alhakin kai harin na Chochin St Theresa a garin Madalla dake kusa da Abuja.
Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe
.