Jamus: Za a kada kuri'ar yanka kauna a Fabarairu
November 12, 2024Ana sa ran shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz zai kira zaben yanke kauna ga gwamnatinsa ko akasin haka a majlisar dokokin kasar ta Bundestag ranar 16 ga watan Disamba mai kamawa, wanda zai share fagen gudanar da zaben kafin wa'adi. Rushewar gwamnatin mai hadakar jam'iyyu uku ta samo asali ne lokacin da shugaba Olaf Scholz ya kori ministan kudi Christian Lindler na jam'iyyar FDP mai sassaucin ra'ayi, dalilin da ya sanya jam'iyyar janyewa daga gwamnatin hadin gwiwar, lamarin da ya janyo gwamnatin Mr Scholz ta rasa rinjaye a majalisar Bundestag. Shi dai Christian Lindner, ya bukaci a yi sauye-sauye a fannin tattalin arziki, amma sauran jam'iyyu biyu na kawancen gwamnatin Jamus na adawa da wannan mataki. Wannan rikicin siyasa na zuwa ne a daidai lokacin da tattalin arzikin Jamus ke tafiyar hawainiya, duk da kasancewarsa mafi karfi a nahiyar Turai.
A zaben da aka gudanar na shekarar 2021, jam'iyyar SPD ce ta samu jagoranci a majalisar dokoki ta Bundestag, wadda a baya take cikin hadin gwiwar gwamnatin da Angela Merkel ta shafe tsawon shekaru 16 tana jagorantar Jamus. Rolf Muetzenich shi ne jagoran jam'iyyar SPD a majalisar dokokin ta Bundestag, ya yi tsokaci kan wannan dambawar siyasar Jamus da ke kara daukar hankalin duniya.
''Game da batun rushe wannan majalisa, mun yanke shawar daukar matakai kamar haka, a ranar 11 ga watan Disamba mai zuwa shugaban gwamnati zai rubuta wa majalisa bukatar jin ra'ayi kan batun yanke kauna kan gwamnatinsa ko akasin haka. A ranar 16 ga Disamban kuma za a tafka muhawara kan kudurin kai tsaye. Wannan zai ba mu damar sanin inda muka dosa kan batun neman sabon shugaban gwamnati. Kuma hakika Olaf Scholz ta taka muhimmiyar rawa a mulkinsa na shekaru uku masu tsauri don ciyar da kasar gaba. Mun taimaki Ukraine sakamakon mamayar da take fuskanta daga sojojin Rasha, mun samar da daidaito ga tattalin arzikin Jamus, inda muka taimaki al'umma.''
Wannan dai wata gaba ce ga jam'iyyar ADF mai tsattsauran ra'ayi da kyamar baki, da ke fatan amfani da damar wajen kara samun karbuwa a siyasar Jamus, kamar yadda jagorar jam'iyyar Alice Wieldel ke tsokaci a kai. ''Mun shaida wasu kwanaki da aka shiga cece-kuce iri-iri kan batun kada kuri'ar yankan kauna ga gwamnati mai ci, har ma aka tsayar da lokacin zabe, wannan wata alama ce kan yadda ake mulkar jama'ar kasa a kaikaice tsawon shearu uku , ya kamata ma a hanzarta kada wannan kuri'a, idan da hali ma a janyo lokacin kusa, kai hatta zaben gama-garin da tsara gudanarwa cikin watan Fabarairun badi kamata ya yi a dawo da shi kusa kusan nan, don yin abin da ya dace''.