An rantsar da sabuwar gwamnati a Holland
July 2, 2024An rantsar da tsohon shugaban hukumar leken asirin Holland Dick Schoof a matsayin sabon firaministan kasar, domin jagorantar gwamnatin hadaka ta masu matsanancin ra'ayin mazan jiya wacce za ta aiwatar da sabbin tsare-tsare mafi tsauri a game da bakin haure masu neman mafaka.
Wannan na zuwa ne dai watanni bakwai bayan gagarumar nasarar da jam'iyyar masu ra'ayin rikau ta samu a zaben kasar, lamarin da ya bai wa Mista Schoof damar gajiyar tsohon firaminista Mark Rutte wanda aka nada a matsayin sakataren kungiyar tsaro ta NATO.
Tuni ma Dick Schoof ya gabatar da sabbin ministocin gwamnatin tasa ga sarkin Willem-Alexander a fadar masarautar kasar da ke birnin Hague inda ko wannen su ya yi mubaya'a ga basaraken.
Siyasar kasar Holland ta sauya sheka ne a daidai lokacin da jam'iyyu masu ra'ayin rikau ke kara karfi a nahiyar Turai inda ko da a baya-bayan nan jam'iyyar NR ta Marine Le Pen ta yi nasara a zaben 'yan majalisar dokokin Faransa.