1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An rantsar da sabon shugaban ƙasar Saliyo

September 18, 2007
https://p.dw.com/p/BuB3

A ƙasar Saliyo an rantsar da madugun adawa Ernest Bai Koroma a matsayin sabon shugaban ƙasa bayan da jamíyar sa ta lashe zaɓen da aka gudanar a kwanakin baya. A jawabin sa jim kaɗan bayan da aka rantsar da shi, Ernest Koroma yayi alƙawarin ba sani ba sabo wajen yaƙi da cin hanci da rashawa da yayi wa ƙasar katutu. Sai dai a yayin da yake wannan jawabi wasu ɗaruruwan jamaá suka afkawa hedikwatar jamíyar mai mulki inda suka riƙa kwasar ganima. Sun kwashe dukkan kayayyakin dake cikin ofisoshin waɗanda suka haɗa da keken rubutu, tebura da kujeru kafin yan sanda su tarwatsa su da barkonon tsohuwa. Yan sanda sun kama wasu daga cikin masu kwasar ganimar sai da wasu rahotanni sun ce mutum ɗaya ya rasa ran sa a lokacin da yan sandan suka buɗe wuta.