1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An rantsar da saban shugaban kasar Zambiya

September 23, 2011

Magoyan bayan Michael Sata madugun adawar Zambiya na nuna farin ciki bayan rantsar da shi a matsayin saban shugaban kasa.

https://p.dw.com/p/12fd3
Magoya bayan Michael Sata na murnaHoto: dapd

An rantsaar da madugun 'yan adawan ƙasar Zambiya Michael Sata a matsayin sabon shugaban ƙasar, bayan nasarar da ya samu a zaɓen ƙasar, inda ya kada shugaba Rubiah Banda wanda jam'iyarsa ta yi shekaru 20 tana mulkin ƙasar.Sata ya samu kashi 43 yayin da Banda wanda ke kan mulki ya samu kashi 36. Sabon shubagaban ya yi alƙawarin kyautata rayuwar talakawan ƙasar. Sata yace ana maraba da masu zuba jari daga ƙetare muddin za su mutunta dokokin kwadungun ƙasar. Sata ya samu goyon bayan yankunan da ake haƙar ma'adinai inda yake zargin kamfanonin China da ci da gumin talakawan yankin.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Yahouza Sadissou Madobi