An miƙa Gbagbo ga kotun ICC a birnin Hague
November 30, 2011Lauyoyin tsohon shugaban ƙasar Ivory Coast Laurent Gbagbo sun ce an danƙa shi ga kotun ƙasa da ƙasa dake Hague domin fuskantar shari'a. Dama dai tuni kotun ta bada sammacin kamo Laurent Gbagbo. Hakan dai ya sanya Gbagbo ya kasance tsohon shugaban ƙasa na farko da aka gabatar gaban kotun ta ICC mai shari'ar manyan laifuka. A shekarar da ta gabata Gbagbo ya ƙi amincewa da shan kaye daga Alassane Outtara bayan zaɓen shugaban ƙasar da ya gudana. Ƙasar ta Ivory Coast dai ta faɗa yaƙin basasa wanda ya yi sanadiyar mutuwar dubban jama'a. A ƙarshe an hamɓarar da Gbagbo daga karagar mulki tare da tallafin dakarun sojin ƙasa da ƙasa. An zargi sojoji dake goyon bayan ɓangarorin biyu na Laurent Gbagbo da Alassan Ouattara da aikata ta'asa akan 'yan Ivory Coast a lokacin yaƙin. Wani babban jami'i na hannun daman Gbagbo Abdon Georges Bayeto yace basu amince da halascin kotun ta ƙasa da ƙasa ba kuma a wajen su har yanzu Gbagbo shine shugaban ƙasar Ivory Coast. " Yace makirci ne na ƙasa da ƙasa aka yiwa Gbagbo, wannan shine abin da yake faruwa, kuma shugaba Laurent Gbagbo ya faɗa cewa bai yarda da halascin kotun ta ƙasa da ƙasa ba, har yanzu kuma shine shugaban ƙasa, abin da yake magana shine a sake ƙidaya ƙuri'un da aka kaɗa".
Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Umaru Aliyu