An miƙa batun Shugaban Sudan ga Kwamitin Sulhu
March 10, 2015Talla
Kotun duniya da ke hukunta masu manyan laifukan yaƙi da ke birnin Hague na ƙasar Netherlands, ta ce ƙasar Sudan ta ƙasa cafke Shugaba Omar al-Bashir da ake zargin da kisan kare dangi da laifukan yaƙi. Kotun ta miƙa lamarin wa Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.
Kotun tana neman Shugaba Bashir ya amsa tuhuma kan laifukan da aka aiwatar a Lardin Darfur na yammacin ƙasar Sudan daga shekara ta 2003, abin da ya yi sanadiyyar hallaka mutane 300,000. Yana fuskantar tuhuma bisa kisa, da gallaza wa mutane, da kisan kare dangi gami da hare-hare kan fararen hula.
Shugaba Omar al-Bashir ke zama mutum na farko da yake kan madafun iko da kotun ta duniya ta ba da sammacin kama shi.