Indiya ta kare kan ta kan kabilar Rohingya
January 3, 2019Talla
Kabilar Rohingyan da jami'an tsaron Indiya suka mika wa hukumomin Kasar Myanmar sun hada da mata da maza wadanda suke tsare a Indiya tun shekara ta 2014 bayan samunsu da laifin kutsawa cikin kasar ta barauniyar hanya,kafin wannan lokaci dai hukumomin Indiya sun mayar da rukunin farko na Rohingya a watan Oktober shekarar bara, Kabilar ta Rohingya da yawansu ya kai kusan dubu 700 sun tsinci kai a tsaka mai wuya tun daga lokacin da suka tserewa kisan da Sojojin kasarsu ke yi musu.