An mayar da Nelson Mandela a asibiti
June 8, 2013Talla
Labaran da muke samu yanzun nan daga garin Pretoria na Afrika ta Kudu na cewar an sake kwantar da tsohon shugaban Afirka ta Kudun Nelson Mandela a asibiti sakamakon matsala da ya sake fusktanta da huhunsa. Fadar gwamnatin kasar ta Afirka ta Kudu ta ce da gabannin wayewar garin yau ne aka rugu da Mandela asibiti bayan da jikinsa ya yi tsanani.
Mahukuntan na Afirka ta Kudu dai sun ce Mandela na cikin wani hali sai dai likitoci na nan na ta kokarin shawo kan wannan matsala da tsohon shugaban dan shekaru casa'in da hudu da haihuwa ke fuskanta a halin yanzu.Wannan dai shi ne karo na biyu da aka kwantar da dattijon cikin makonni takwas din da su ka gabata kan wannan matsala.
Mawallafi : Ahemed Salisu
Edita : Usman Shehu Usman