1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kwantar da Mandela a asibiti

March 28, 2013

Rahotanni daga Afrika ta Kudu na cewar an sake kwantar da tsohon shugaban kasar Nelson Mandela a asibiti biyo bayan matsala da ya sake samu a huhunsa.

https://p.dw.com/p/186Lj
Former South African President Nelson Mandela smiles at home in Houghton, after casting his vote, in this May 16, 2011 file photo. Mandela was admitted to hospital on February 25, 2012 for treatment for a "long-standing abdominal complaint", the government said. REUTERS/Elmond Jiyane/GCIS - Government Communication and Information System/Handout/Files (SOUTH AFRICA - Tags: POLITICS) FOR EDITORIAL USE ONLY. NOT FOR SALE FOR MARKETING OR ADVERTISING CAMPAIGNS. THIS IMAGE HAS BEEN SUPPLIED BY A THIRD PARTY. IT IS DISTRIBUTED, EXACTLY AS RECEIVED BY REUTERS, AS A SERVICE TO CLIENTS
Symbolbild Nelson MandelaHoto: Reuters

Shugaban kasar Afrika ta Kudu JAcob Zuma wanda ya tabbatar da kwantar da Mr. Mandela a asibiti ya ce an kai shi ne da tsakar daren jiya Laraba sai dai shugaban bai bayyana asibitin da aka kwantar da Mandelan ba.

Da ya ke karin haske game da rashin lafiyar ta Mandela, kakakin shugaban kasar ta Afrika ta Kudu Mac Maharaj ya ce likitoci na duba tsohon shugaban kuma su na kokarin tabbatar da cewar ya samu kulawa ta musamman.

Mr. Mahraj ya kuma kara da cewar shugaba Zuma ya yi masa fatan samun lafiya cikin kankanin loakci kana ya na da da tabbacin cewar likitocin da ke kansa za su yi aiki sosai wajen tabbatar da cewar ya samu lafiya. 

A dan tsakanin nan dai tsohon shugaban na kasar Afrika ta Kudu dan shekaru 94 da haihuwa ya yi ta fama da larurori musamman ma dai na cutar huhu wanda ta sanya shi kwanciya a asibiti cikin watan Disambar shekarar da ta gabata inda aka yi masa maganin cutar ta huhu baya ga wata kwarya-kwarya tiyata da aka yi masa.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Usman Shehu Usman