1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An dakile harin kunar bakin wake

Ramatu Garba Baba
June 3, 2019

Jami'an tsaro sun sanar da dakile wani yunkurin wasu 'yan kunar bakin wake 4 da suka yi niyyar kai hari a katafaren kamfanin mai na Sonidep da ke a jahar Diffa a gabashin Nijar.

https://p.dw.com/p/3Jlyb
Nigeria Armee Task Force gegen Islamisten Boko Haram
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Wani jami'in gwamnati da ya sheda aukuwar lamarin a tattauna da kafar yada labaran Faransa AFP, ya kara da cewa, akwai wasu da  aka kama, sun kuma fallasa kansu inda suka baiyana shirinsu na kai hari kan wani karamin coci da ke yankin, an gano abubuwan fashewa a mabuyarsu inji jami'in.

 Diffa da ke gabashin jamhuriyar Nijar, al'ummarta ba su zarta dubu dari biyu ba, amma ta fuskanci tarin hare-hare daga mayakan Boko Haram da ya janyo asarar rayuka tare da tilastawa da dama zama 'yan gudun hijira.