An kashe jami'an sa kai a Kenya
May 12, 2021Talla
Mayakan Al-Qaeda da na Al-Shabaab dai sun kai hari ne ga babbar layin waya da ke gudummar Mandera yayinda suka yi yunkurin kai wani harin a gundummar Wajir.
Kungiyar Al-Shabab dai ta sha alwashin daukar fansa kan Kenya saboda tura wa da dakarunta Somaliya don yakar masu tada kayar baya. Dakarun na Kenya dai suna yaki tukuru a Somaliya tun daga shekarar 2011, lokacin da aka tura su biyo bayan garkuwa da Turawa na ta'azarra a kasar wanda aka daura alhakin hakan ga mayakan.