An kashe gomman 'yan Boko Haram a Najeriya
November 20, 2024Rahotannin da ke fitowa daga Najeriya, na cewa an kashe wasu mayakan Boko Haram su kimanin 50, yayin kuma da wasu jami'an hukumar tsaro ta farin kaya su takwas suka bata.
Lamarin ya faru ne a lokacin da 'yan Boko Haram din suka yi wa motocin jami'an tsaron kwanton bauna, a yayin da suke sintirin kare manyan na'urorin samar da wutar lantarki a jihar Neja da ke a tsakiyar Najeriyar.
Mai magana da yawun hukumar tsaro ta farin kayan, Babawale Afolabi ya ce kimanin 'yan Boko Haram din su 200 ne suka yi wa ma'aikatansu tsinke a lokacin da lamartin ya faru.
Koda yake kungiyar Boko Haram ta yi kaurin suna a yankin arewa maso gabashin Najeriya, hukumomi na cewa suna da sansanoni a jihar Neja, kuma kafin yanzun suna mai kai wa barikokin soja da ma yankunan fararen hula hare-hare.